Shaikh Yahya Hasan ya gabatar da jawabi ne akan dalilin da ya sanya yan Shi’a su ke raya al’amarin Imam Husaini musamman ma shahadarsa. Inda ya bayyana cewa wanna sunna ce data samo asali tun daga kan Manzon Rahama(S) har ta gangaro zuwa kan sauran A’imma da sauran Annabawan Allah Ta’ala (Alihimussalam). Dukkaninsu sun tuna da kisan Imam Husaini tare da yin kukan shahadarsa.
Zaman ya samu halartar al’umma daga ciki da wajen Da’irar, inda su hada da wakilin yan uwa na Da’irar Gwaram tare da waikilin yan uwa na Da’irar Alkaleri da sauran yan uwa.
Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
22/6/2026R
Your Comment